Gamayyar Ƙungiyar mutan arewacin Najeriya CNG ta ce cafke jagororin kungiyar Inyamurai da Yarbawa Nnamdi Kanu da kuma Sunday Igboho ba shine mafita ga matsalolin da ake ciki ba.
Kungiyar ta ce mafita guda daya ga matsalar wadannan yab aware kawai shine a gudanar da zaben raba gardama.
Shugaban kungiyar Abdulaziz Suleiman ya ce kama wadannan mutane biyu babu abinda zai haifar face rura wutar wannan rikici.
“Mun san cewa yunkurin ɓallewa daga wata kasa mugun kaba’ir wanda ba kowace gwamnati ba ce za ta zura idanu tana kallo, amma kuma zaman sasantawa ya fi”
Idan ba manta ba a makonni da suka gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da cewa ta cika hannu da Nnamdi Kanu, yayin da shi kuma kanwa uwar gami Sunday Igboho aka sanar da cafke shi a ranar Talata.