By Ishaq Dabai
Kungiyar likitocin Najeriya NMA, a ranar Alhamis tayi Allah wadai da mummunan kisan da aka yiwa daya daga cikin membobinta, Dokta Chike J Akunyili, matar marigayi Farfesa Dora Akunyili, tsohon Darakta Janar na Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa, NAFDAC, tana kira ga Hukumomin Tsaron Najeriya dasu zakulo wadanda suka aikata laifin.
A cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai wanda Sakataren Yada Labarai na NMA na kasa, Dakta Aniekeme Uwah ya sanya wa hannu ya bayyana lamarin a matsayin “mutuwa daya tayi yawa”, ya kuma bukaci gwamnatin Tarayya da na Jihohi dasu cika babban nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya basu na kare rayuka da kadarori na dukkan ‘yan Najeriya.
Sanarwar mai taken “Mutuwa Daya Yawa, Munyi Kuka Don Najeriya” tana karanta cewa “NMA tana matukar bakin cikin kisan gillar da aka yi wa wani daga cikin membobinta, Dr Chike J Akunyili yayin da kungiyar ke jiran sanarwa a hukumance kan binciken da ake yi. rahotannin da aka tattara daga kafafen yada labarai daban daban sun nuna cewa wannan mummunan lamari ya faru yayin da wanda aka azabtar ke kan hanyarsa daga lacca don tunawa da marigayiya Dora.
“Muna kuma rokon hukumomin tsaro dasu yi duk mai yiwuwa wajen ganin an kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin don su zama abin hana wasu.
“Allah ya bamu dangi da kuma duk ‘yan Najeriya karfin gwiwa don jure wannan babban rashi da ba za a iya gyarawa ba. Amin,”in ji Uwah.