Kungiyar kwallon kafa ta Nijeriya ta Super Eagles ce a matsayi na 34 a duniya a Jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya wato FIFA ta fitar inda da Nijeriya tana matsayi na 33.
Hakan ya biyo ne bayan Nijeriya ta yi kunnen doki da kasar Ukraine wato 2 da 2 a wasan sada zumunci da suka fafata. A nahiyar Afrika dai kasar Senegal ce a matsayi na 20 a duniya inda take a matsayi na 1 a nahiyar Afrika.
Ga jerin jadawalin kasashen a nahiyar Afrika wato daga ta 1 zuwa ta 10:
1. Senegal
2. Tunisia
3. Nigeria
4. Algeria
5. Morocco
6. Egypt
7. Ghana
8. Cameroon
9. DR Congo
10. Cote d’Ivoire