Hukumomi a kasar Afghanistan sun bayyana cewa Ƙungiyar mayakan Taliban ta sake kwace iko da babbar iyakar Kasar da Kuma Iran a ranar Juma’a.
Wani faifan bidiyo da ya bayyana, ya nuna yadda mayakan ke kokarin janyo tutocin kasar Afghanistan dake ofishin hukumar hana fasa-kwauri.
Kungiyar ta Taliban na ci gaba da cin karenta babu babbaka bayan da da kasar Amurka ta janye sojin ta na Kundum bala a kasar ta Afghanistan.
Da ma dai ta bayyana cewa tuni ta karɓe iko da kashi 85 na manyan biranen kasar, ikirarin da gwamnati ta bayyana a matsayin tatsuniya.