Shugaban Kungiyar Yarbawa ta Afenifere Mista Yinka Odumaki ya mutu a yau Asabar 3/4/2021.
Rahotanni sun yi nuni da cewa Odumaki ya mutu ne a babban asibitin koyarwa na Jihar Legas sakamakon cuta Mai kama da COVID-19 wato Korona.
Mai dakin Shugaban Yarbawan wacce mai rajin kare hakkin dan Adam ce Dakta Joe Okei-Odumakin ta tabbatar da mutuwar mai gidan nata inda lokacin hada wannan rahoto ta ce tana hanyar zuwa asibitin ne.
“Yinka ya yi bankwana da duniya, mun gana da shi a gidan yari amma yanzu ba ya cikin mu a duniya” ta bayyana a cikin harshen yarbanci.
“Jaridar Leadership ta yi kokarin jin ta bakin shugancin Ƙungiyar Afenifere amma ya ci tura.