By Abbas Yakubu Yaura
Wani mai suna Reprieve yazo da wata yarinya mai shekaru 16 mai suna Joy Abahi Amuh wadda ta samu mafi kyawun sakamakon jarabawar WAEC a shekarar 2020 a jihar Benue a matsayin wata kungiya mai zaman kanta data ba ta Naira 500,000 don samun damar ci gaba da karatun ta.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Joy ta sami makin “A” a duk darussa tara da ta rubuta a makarantar sakandare ta St Paul, Otukpo a Jarabawa WAEC.
Sai dai kuma rashin kudi ya hana ta yin jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandare (UTME) na shekarar 2021, hakan ya sa ta dauki matakin koyarwa a makarantar firamare Reno domin ta samu damar ajiye kudi da zata ci gaba da karatun ta.
A yayin da take koyarwa, ta zo ne kwanaki kadan da wata kungiya mai zaman kanta ta (ESLF), tare da hadin gwiwar (BIPC), inda ta ba ta kyautar tsabar kudi Naira 500,000 a matsayin ” Mafi kyawun Dalibi ”a cikin jihar a 2020.
Manajan Darakta na BIPC, Barista Alex Adum, ya ce kyautar ta dace da kuma cancanta don taimakawa wajen neman ilimi.
Sannan ya ce, “Mun zabi gudanar da wannan karramawar ne domin karfafa ƙwazo a fannin koyo da aiki tuƙuru a tsakanin matasanmu masu tasowa.
Kazalika Joy wacce ta fito daga unguwar Igaluwa dake gundumar Ugboju a karamar hukumar Otukpo ta jihar, ta halarci makarantar firamare ta RCM, Ipom-Ugboju, sannan ta wuce makarantar sakandare ta St Paul, Otukpo.
Shugaban makarantar St Paul, Mista Peter Emaikwu ya ce Joy daliba ce mai kwazo da mai da hankali akan karatunta.