Wasu mambobin gamayyar kungiyoyin fararen hula a Arewacin Nigeria, sun bukaci babbar kotun tarayya dake Abuja da ta umarci majalisar dokoki ta Kasa ta zartar da wata doka da zata Kori Yan yankin Kudu maso gabashin Kasar daga Nigeria.
Wadanda suka jagoranci shigar da wannan bukata sun Hadar da Nastura Ashir Shariff, Balarabe Rufa’I, Abdul’azez Sulaiman da kuma Aminu Adam, inda suka Bayyana hakan da cewa shine zai taimaka wajen samun nasarar Kan Yan awaren da ke rajin kafa haramtacciyar Kasar Biafra.
Sun kuma Kara da cewa abun da ya suka shigar da wannan korafin, basa son yakin da maimai ga yakin da ya faru a shekarar 1967 zuwa 1970 Wanda ya haddasa asarar rayukan Yan Kasa baya ga dubban miliyoyi da suka salwanta.
To Sai dai anasu bangaren Yan yankin da aka bukaci a kore su daga Nigeria, an hango wasu lauyoyi masu mukaman SAN, Chuks Muoma, Ukpai Ukairo, Ebere Uzoata da Obi Emuka Suma da suke Bayyana gaban kotun da nufin kare wadanda ake Kara, tare da bukatar kotun ta sahale musu domin tsayawa yankin.
Cikin takardar da suka gabatar ta hannun Victor Onweremadu sun Bayyana cewa cire yankin Kudu maso gabas daga Nigeria, wani abu ne da zai haifar da illa ga rayuwar al’ummar Igbo, Dan haka kuma zasu tabbar da cewa al’ummar su sun Sami yancin da ta Kamata.