Kungiyoyin ma’aikata a jami’o’i wadanda ba koyarwa suke ba, a ranar Laraba sun gargadi gwamnatin tarayya akan ka da su haddasa rikici da rigima a makarantun bisa zargin gwamnatin da sanya son rai da fifita wani bangare a yayin rabon naira biliya 40 na alawus din ma’aikatan da gwamnatin take shirin yi.
Wannan gargadin ya fito ne daga bakin kungiyoyi uku da suka hada da SSANU, NASU, da kuma NAAT awanni kadan bayan da ASUU suka janye yajin aikin da suka kwashe wata Tara suna yi.
Ma’aikatan sun yi barazanar cewa ba za su koma aiki ba har sai gwamnati ta gyara abin da suke zarginsu da shi. Inda suka ce gwamnati ta bai wa ASUU kashi 75 na alawus, su kuma aka bar su da kashi 25.
Comrade Ibeji Nwokoma, shugaban kungiyar NAAT ya ce; duk wanda yake tunanin ma’aikatan da ba koyarwa suke ba za su koma jami’a su ci gaba da ayyukansu bisa abin da ya faru, to mafarki ake yi, har sai gwamnati ta gyara zargin da suke mata.
Ya ce kungiyarsu na yin dukkanin mai yiwuwa domin zama da Sakataren ma’aikatar Kwadago da samar da ayyukan yi, domin shaida masa wannan matsalar.
Shima shugaban kungiyar SSANU, Kwamared Mohammed Haruna Ibrahim ya ce abin da gwamnati ta yi ya nuna ba ta son zaman lafiya a cikin jami’o’in, inda ya ce kungiyarsu ba za ta dauki abin da wasa ba.