Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain mai barin gado Lionel Messi ya samu tayi daga manyan kungiyoyin nahiyar turai guda biyu a cikin sa’o’i kadan da suka gabata.
Makomar Messi ta zo karshe bayan ya buga wasansa na karshe a PSG da suka fafata da Clermont Foot ranar Lahadi.
KU KARANTA: An Kuma: Majalisar Dokokin Wata Jiha Ta Dakatar Da Wani Shugaban Karamar Hukuma
Kulob din Barcelona da Al-Hilal ne ke kan gaba a zawarcin dan wasan, yayin da Inter Miami ta ce ta yi gagarumin yunkuri a cikin ‘yan sa’o’i da suka wuce domin mallakar dan wasan.
Sai dai a cewar dan jarida Pablo Gravellone, yanzu Messi ya samu tayi biyu daga Chelsea da Newcastle United.
Kungiyoyin Premier biyu na sa ido kan halin da dan wasan na Argentina yake ciki.
Gabatowar gasar Premier kuma na iya kasancewa kan ta tilasta su zawarcin dan wasan, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau bakwai.
A wani labarin kuma: Kwankwaso Ya Yi Magana Akan Tsohon Sarkin Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya mika sakon ta’aziyya da godiyarsa ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya wanda ya rasu
a watan Yunin 2014.
Sarkin wand guda ne cikin shugbannin addinin musulinci da ake girmamawa, kuma mai sukar mayakan Boko Haram.
Ya rasu yana da shekaru 83 a watan Yunin 2014 bayn ya yi fam da rashin lafiya jim kadan bayan ya dawo daga Landan, inda yake jinya.