Ma’aikatan jami’o’i na Nigeria za su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar Juma’a sakamakon yadda FG ta ke rikon sakainar kashi ga tsarin biyan albashi na IPPIS, da kuma rabon N40bn na alawus alawus tare da kuma gaza biyan kudaden hutu da sauran hakkoki na albashi mafi karanci.
Tuni da kwamitin ma’aikatan jami’o’in na kasa, da suka hada da kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i SSANU, da kuma ma’aikatan manyan makarantun ilimi NASU, suka aikewa dukkanin rassansu takardar umurnin fara yajin aikin a ranar Juma’a.
Kwafi na takarar dauke da sa hannun shugaban kungiyar SSANU, Mohammed Ibrahim da babban sakataren kungiyar NASU, Prince Peters Adeyemi, an aike wa manema labarai a ranar Alhamis.
Idan za a iya tunawa, kwamitin JAC ya sanar da cewa kungiyoyin za su shiga yajin aikin sai baba-ta-gani daga ranar 5 ga watan Fabreru 2021 sakamakon gazawar gwamnatin tarayya na biyawa kungiyoyin bukatunsu.
Sauran bukatun kungiyoyin ya hada da rashin biyan kudaden ritaya ga tsoffin ma’aikatan jami’o’i, rashin kafa kwamitin kai ziyara ga jami’o’i, karancin kudaden da ake warewa jami’o’i, nuna fifiko akan malaman jami’o’i akan ma’aikatan da ba malamai ba, da dai sauransu.