Daga: Abbas Yakubu Yaura
Labarin wata yarinya da mahaifanta – ita dai wannan yarinya an haifeta annan kasar Najeriya amma saboda iyayenta masu karfine sai suka tafi da ita kasahen turawa inda tayi karatunta acan hartakai ga tashiga jami’a wanda hakan yasa iyayenta da zasu dawo gida najeriya suka barota acan kasar turawa.
A kwana atashi yarin tagama karatu,zata taho gida sai tafara tunanin abin da zata tahowa da iyenta na tsaraba wanda zai sa su mamaki,tana cikin wannan tunani sai ta sami labarin wani ruwa da duk wanda ya shashi to nan take zai dawo saurayi idan na mijine idan kuma mace ce zata dawo budurwa fil a leda,
Aikuwa taje ta debo ruwannan ta taho musu dashi bayan tasauka a najeriya taje gida ta huta sai ta fadawa mahaifiyarta cewa aiko tataho musu da mai da tsohuwa yarinya ta dauko mata ruwa tace gashi kiyi kurba daya tanayi ta dawo budurwa.
Sai tace idan baba yadawo kibashi shima yayi kurba daya daga haka karyakara, nizanfita wajen nasha iska.
Bayan tafitane sai mahaifinta yadawo gida, dawowar sa keda wuya sai yaga abin mamaki yake tambayar matar tasa meke faruwane,sai yatafi da gudu danufin ya rungumeta sai ta dakatar dashi tace ka yimin tsufa bazaka tabani a hakaba sai kadawo sauri.
Sai yace da ita to tayaya? Sai tace dashi yanzu kuwa sai ta dauko ruwannan tace masa gashi tsarabar ‘yar muce da tataho mana da ita daga Turai.
Sai ta gargade ni da cewar “na fada maka cewa kurba daya zaka yi daga haka karka kara.”
“Aiko nan take ya karba maimakon yayi kurba daya sai ya shanyedu yana shanyewa yakoma jariri sai abin yabata mamaki,sai budurwar matar tasa tadaukeshi tagoye abaya.
Anacin haka sai yar tadawo tace da mahaifiyar tata a ina kika samu jariri saitace da ita babankine ya shanye ruwandu yakoma jariri.