By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki.
Shekarau ya koma jam’iyyar NNPP ta tsohon sanata Kwankwaso.
Tsohon Darakta Janar na kungiyar goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu, AbdulMumin Jibrin, ya bayyana hakan a shafin sa na Twitter.
Sanarwar ta Tweet ta bayyana cewa, “Da Dumi-duminsa- Sanata Ibrahim Shekarau ya koma NNPP. Cikakkun bayanai zasu zo daga baya.”
Daga baya, jam’iyyar ta wallafa hotunan ziyarar da shugaban jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, ya kai gidan Shekarau a twitter.
” Injiniya Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar taya murna ga tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau a yau bayan ya sauya sheka zuwa NNPP,” in ji jam’iyyar.
Shekarau yana wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa.
Sanatan mai shekaru 66 a duniya ya kasance tsohon ministan ilimi na Najeriya kuma ya yi mulkin gwamnan jihar Kano a karo na biyu a jere.
An zabe shi a watan Afrilun shekarar 2003 kuma an sake zabe a watan Afrilun shekarar 2007.
Ya kasance daya daga cikin ‘yan takarar da suka yi burin zama shugaban kasa a babban zaben Najeriya na shekarar 2011.