Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce mutane 1,955,657 ne ake sa ran za su shiga zaben gwamnan jihar Osun a ranar 16 ga watan Yuli.
Kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu kada kuri’a na kasa, Mista Festus Okoye ne ya bayyana haka a wani taron tattaunawa da shugabannin kafafen yada labarai da aka yi yau Juma’a a Osogbo.
Okoye ya ce jam’iyyun siyasa 15 ne za su shiga zaben a dukkan kananan hukumomin jihar 30.
Kamar yadda hukumar ta INEC ta wallafa, dukkan ‘yan takarar gwamna maza ne, yayin da shida daga cikin mataimakan gwamna mata ne.
‘Yan takarar da aka lissafa sune Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC, wanda shine gwamnan jihar mai ci; Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP da Omigbodun Akinrinola na jam’iyyar SDP.
Sauran sun hada da Lasun Yusuff na Jam’iyyar LP; Adesuyi Olufemi ZLP; Adeleke Adedapo BP; Adebayo Elisha APP; Awoyemi Lukman APM; Awojide Segun AAC; Akinade Ogunbiyi Accord; Kehinde Atanda ADP; Rasaq Saliu NNPP; Ayodele Adedeji na jam’iyyar (PRP) da Ademola Adeseye na jam’iyyar matasa YPP.
Sai dai ya bukaci shugabannin kafafen yada labarai na jihar da su tabbatar da sahihancin rahotanni a lokacin zaben gwamna. Okoye, wanda ya kara da cewa kafafen yada labarai na da matukar muhimmanci ga tsarin zabe, ya ce idan ba ‘yan jarida ba, tsarin zabe da tsarin hukumar ba zai iya kaiwa ga masu zabe da ‘yan takarar jam’iyyu ba.