Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta kasa NARD a ranar Litinin ta ce mambobinta a jihar Abia sun shafe kusan shekara guda suna yajin aiki saboda rashin biyansu albashi.
Shugaban kungiyar, Dokta Dare Ishaya ne ya bayyana haka a wata hira da gidan talabijin na Channels Television a cikin shirin Sunrise Daily.
Ya caccaki gwamnatin jihar Abia kan yadda likitoci masu neman kwarewa a jihar ke bin su albashi tare da gazawa wajen aiwatar da dokar koyar da likitoci masu neman kwarewa a jihar.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Ishaya ya bayyana cewa ana ci gaba da tsare-tsare tare da gwamnan jihar Okezie Ikpeazu, wanda ya amince ya biya bashin albashin watanni bakwai da kuma kafa dokar a Kudu maso gabashin jihar.
“Ina so in shaidawa ‘yan Najeriya cewa jihar Abia, likitocinmu na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Abia sun shiga yajin aiki kusan shekara guda izuwa yanzu,” in ji shi.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/da-dumi-dumi-kungiyar-asuu-ta-tsawaita-yajin-aikin-da-ta-keyi/
“Duk da haka an sami ɗan ci gaba kaɗan. A karshen taron da kungiyar likitocin masu neman kwarewa suka yi da gwamnan da wakilanmu, an amince da cewa gwamnan a shirye yake ya saki bashin albashin watanni bakwai a cikin mako guda sannan kuma ya kafa dokar koyar da likitoci masu neman kwarewa a jihar.”
Idan gwamnatin jihar ta yi murabus a nata bangaren, Shugaban NARD ya ce majalisar zartaswa ta kasa za ta yi nazari kan komai tare da daukar matakin da ya dace a cikin makonni biyu masu zuwa.
Ya yabawa Gwamnonin Ifeanyi Okowa (Delta), Babajide Sanwo-Olu (Lagos), Abdullahi Sule (Nasarawa), Samuel Ortom (Benue), Babagana Zulum (Borno) da Mai Mala Buni (Yobe) kan zuba jarinsu a fannin kiwon lafiya.
Ishaya ya kuma yi kira ga sauran gwamnonin jihohi da su yi koyi da wadanda suka yi kokarin inganta harkar kiwon lafiya a yankunansu.
Likitocin suna rokon gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan biyan sabon asusun horas da likitoci masu neman kwarewa (MRTF) domin mambobinta su hadu da ranar rufe rajistar jarrabawa kamar yadda kwalejin kula da lafiya ta kasa (NPMCN) ta tallata.
Suna kuma neman a gaggauta aiwatar da kuma biyan sabon alawus na hatsaru da basussukan da ke ƙunshe a cikin da’ira daga Hukumar Kula da albashi, kudin shigar Ma’aikata ta Ƙasa (NSIWC).
Sauran bukatun sun hada da biyan basussukan 2014, 2015 da 2016 ga mambobi da suka cancanta da kuma biyansu nan take na gyara mafi karancin albashi ga mambobin kungiyar da ba su amfana ba tun bayan aiwatar da shi shekaru da dama da suka gabata.
Likitocin dai na bukatar a gaggauta yin nazari a kan tsarin albashin likitocin (CONMESS) da sauran alawus-alawus masu alaka da su idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki a halin yanzu, sannan kuma bisa sharuddan da aka amince da su daga yarjejeniyar hada-hadar kudi ta baya (CBA) cewa ya kasance ana bibiyartaakai-akai.