• Mutun uku aka tura gidan gyaran hali na Kirikiri, bisa zargin fashi da makami.
• Wata Kotu da ke birnin Ikeja ce, ta yanke wannan hukuncin ga mutanan.
• Kotun ta kuma da ge sauraran karan izuwa ranar 19 ga watan Yulin shekarar nan, domin cigaba da gudanar da bincike
A ranar litinin wata Kotu dake birnin Ikeja ta bada umarnin kai wasu mutun 3 gidan gyaran hali, bisa zargin su da fashi da makami.
Rundunar yan sandan jihar, ta zargi Yusuf Hussain mai shekara 23, da Ibrahim Yakubu mai shekara 31, da Muktar Suleiman mai shekara 25, da laifin fashi da makami, da kuma rike bindigu ba bisa ka’ida ba.
Mai shari’ar kotun Mrs O.O Fajana, wacce ta ki amince wa da rokon da wadanda ake zargin su ka yi, ta bada umarnin garkame su a cibiyar gyaran hali na Kirikiri dake jihar Legas.
Ta kuma bada umarnin kai kundin binciken mutanen, zuwa wajan Daractan kula da wadanda ake bincike DPP, domin sa ke yin dubi kan lamarin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kungiyar yan jarida ta kasa tag gargani gwamna da hukumomin tsaro
Daga bisani Fajana, ta da ge sauraran karan izuwa ranar 19 ga watan Julin shekarar nan.
Jami’in dan sandan me kula da karar ya bayyana wa kotun cewa, an kama wadanda ake zargin ne da, bindiga kiran gida, da kuma adduna.
Ya kara da cewa, laifin na su, ya saba wa sashin doka na 299 da kuma 330 na kundun dokar manyan laifuka na jihar Legas, na shekarar 2015, kamar yadda NAN ta bayyana.
Comments 2