Wata Kotun Majistare da ke Kano a ranar Litinin ta ba da umarnin tsare wani matashi dan shekara 30, Abdullahi Idris, da ake zargi da yin lalata da wani yaro dan shekara 13, a gidan gyaran hali har sai an ba da shawarar kan shari’a.
Idris wanda ke zaune a Sheka Baranda Quarters Kano, ana tuhumar sa ne da laifin yin garkuwa da yaton da kuma wani laifi da bai dace ba.
Alkalin kotun, Mustapha Sa’ad-Datti, ya umurci ‘yan sanda da su mayar da kundun shari’ar Idris zuwa ofishin daraktan kula da kararrakin jama’a na jihar Kano domin samun shawarwari kan shari’ar.
Sa’ad-Datti ya dage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar 2 ga watan Agusta domin karin bayani.
Tun da farko, Lauya mai shigar da kara, Ms Asma’u Ado, ta shaida wa kotun cewa Idris ya aikata laifin ne a ranar 11 ga watan Fabrairun 2022 a Sheka Baranda Quarters Kano.
Ado ya yi zargin cewa da misalin karfe 10 na dare Idris ya yaudari yaron mai shekaru 13 a cikin dakinsa da ke Sheka Baranda Quarters Kano inda ya yi lalata da yaron.
Laifin, in ji ta, ya saba wa tanadin sashe na 272 da 284 na kundin laifuffukan jihar Kano.
Sai dai rahotonni sun bayyana cewa, Idris ya musanta aikata laifin da ake zarginsa da shi.
A wnai labarin kuma na daban.
Shugabannin kungiyar G7 za su tara dala billiyan dari shida don talfawa kasashe masu tasowa
Shugabannin kungiyar G7 sun yi cikakken shirin tattara kudade dala biliyan 600, don samar da kudade ga kasashe masu tasowa, a wani mataki da ake ganin ya sabawa shirin Belt and Road na kasar Sin.
Shirin hadakar kasashen duniya na bunkasa ababen more rayuwa da zuba jari wato The Partnership for Global Infrastructure and Investment (PGII) a turance ya sake ƙaddamar da wani tsari da aka buɗe a taron G7 na bara a Ingila.
An tsara shirin a matsayin wata hanya ta tinkarar babban burin kasar Sin na Belt and Road Initiative (BRI). Inda Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kaddamar da shi a shekarar 2013, domin samar da kudade ga kasashe masu tasowa don gina ababen more rayuwa kamar tashoshin jiragen ruwa, tituna da gadoji.
To sai dai Shugaban Amurka, Joe Biden, ya ce, shirin zai ba da gudummawa ga kowa kasa.
Tun da fari An soki shirin samar da ababen more rayuwa na Tiriliyoyin daloli na kasar Sin da cin bashi mai yawa.
An fara bayyana shirin samar da ababen more rayuwa, a taron G7 na 2021 da aka yi a Biritaniya, wanda ake kira “The Build Back Better World” a lokacin, kuma an canza aikin zuwa The Partnership for Global Infrastructure and Investment, kafin a sake dawo da shi a taron na wannan shekarar ta 2022.
Da yake tsokaci game da hadin gwiwar kasa da kasa, shugaban Amurka Joe Biden, ya ce, shirin na G7 ba taimako ba ne ko sadaka, amma zuba jari ne da zai kai ga kowace kasa.
Ya kara da cewa, tsarin zai baiwa kasashe damar ganin “tabbatacciyar fa’idar hadin gwiwa da dimokuradiyya.
Shirin ya yi kira ga shugabannin G7 da su tara dala biliyan 600 a cikin shekaru biyar don samar da kudaden kaddamar da ayyukan samar da ababen more rayuwa a kasashe masu matsakaita da masu karamin karfi.
Rayhaan Radio ta ruwaito cewa, Amurka ta yi alkawarin tara dala biliyan 200 na jimillar, ta hanyar tallafi, kudaden tarayya da zuba jari masu zaman kansu, yayin da Tarayyar Turai, ta sanar da karin Euro biliyan 300.
A cewar rahotanni, shirin zai kasance da nufin magance sauyin yanayi, inganta kiwon lafiya a duniya, cimma daidaito tsakanin jinsi da samar da kayayyakin aiki na zamani.
Wasu daga cikin tsare-tsaren da aka yi a taron na bana sun hada da aikin samar da hasken wutar lantarki mai amfani da rana a Angola, da cibiyar samar da alluran rigakafi a kasar Senegal, da wata hanyar sadarwa ta karkashin ruwa mai nisan kilomita 1,609 da ta hada Singapore da Faransa ta Masar.
Sai dai shugabar hukumar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta ce makasudin sabon shirin shi ne gabatar da “hanyar zuba jari mai karfi ga duniya don nunawa abokan huldarta a kasashe masu tasowa, cewa suna da zabi”.