A yau juma’a ce wata Kotun Majistiri dake zaman ta a garin Kano, ta bada umarnin cigaba da tsare wani mutum mai suna Mohammed Sani a gidan gyaran hali, bisa zargin yi wa wata budurwa mai fama da tabin hankali Fyade.
Rahotanni sun nuna cewar, budurwar na da shekara 15 me Kuma na fama da lalurar tabin hankali.
Rundunar yan sandar jihar ce ke jagorantar tuhumar Sani Mai shekara 46, dake zaune a Rijiyar Zaki dake cikin garin Kano, kan zargin sa da yiwa budurwar fyade, Wanda ya saba wa sashin doka na 283 na kundun dokar Penal Code.
Kazalika kafin yanke hukuncin Mai gabatar da kara Asma’u Ado ta bayyana wa Kotun cewa, Wanda ake zargin, ya aikata wannan aika-aikan ne a ranar 11 ga watan Yulin Shekarar nan, a yankin Rijiyar Zaki da ke birnin Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mika Abba Kyari: Kotu ce kawai za ta yanke Hukunci, inji Antoni Janar
Ta kara da cewa, da musalin karfe 11 na safe ne, wanda ake zargin ya kai yarinyar mai fama tabin hankali dakin shi, inda ya yi mata fyade.
Anashi bangaren Mohammed Sani ya karyata zargin da ake yi ma shi, a gaban Kotun.
Sai dai Mai shari’an Kotun na Majistiri Mustapha Sa’ad-Datti, ya dage sauraran karar harzuwa ranar 28 ga watan Ogustan shekaran nan, domin cigaba da sauraran karar.