A yau Talata Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da samun rahotannin cutar Kwalara guda 559 a fadin jihar.
Kwamishiniyar kula kiwon lafiya ta jihar Mrs Juliana Bitrus ce ta bayyana hakan, ga manema labarai a garin Maiduguri babban birnin jihar.
Ta kara da cewa, an sami wadanda cutar tayi sanadiyar mutuwar su guda 43 a fadin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan bindiga sun yi garkuwa da Mabiya Cocin Living Faith a Kogi
A cewar kwamishiniyar, an samu rahotannin cutar ne a Kananan hukumomin Gwoza, Kaga, Hawul, Magumeri, Dambao, Birnin Maiduguri da kuma karamar hukumar Jere dake jihar.
Bitrus ta ce, ” An samu rahotannin 354 na cutar Kwalara a karamar hukumar Gwaza, inda mutum 18 suka mutu, ya yin da a kasamu guda 126, da Kuma mutuwar 11 a karamar hukumar Hawul
” Sauran sun hada da na karamar hukumar Kaga inda a kasa mu rahotanni 22, da mutuwar Mutum 2, Magumeri rahotanni 6 da mutuwar Mutum guda, sai na Damboa da aka samu rahotanni 39 da mutuwar Mutum 10, da na Hawul da aka samu rahotanni 8 da mutuwar Mutum guda, da kuma na karamar hukumar Maiduguri da aka Samu rahotanni 4, amma babu mutuwa.” a cewar Kwamishiniyar.
Kazalika kwamishiniyar ta ce, gwamnatin jihar ta kaddamar da wani tawagar gaggawa, da zai yi dubi kan cutar, domin dakile ya duwar ta, a sauran kananan hukumomin dake fadin jihar baki daya.