Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa, ta sami rahotan cutar Kwalara 1,665 a fadin jihar, cikin watan ni biyar da su ka gabata.
Kwamishiniyar kiwon lafiya ta jihar Dakta Amina Mohammed Baloni ce ta bayyana hakan, lokacin da take zanta wa da mane ma labarai a garin Kaduna, a yau Alhamis.
Mohammed Baloni ta bayyana cewa, an sami rahotannin ne tun daga watan Afurilu shekarar nan, zuwa watan Ogustan da muke ciki, a cikin kananan hukumomi 19 dake jihar.
Kwamishiniyar ta kuma alakanta barkewar cutar, da rashin tsaftace Muhalli.
KARANTA WANNAN LABARIN: Obasanjo da Secundus na wata ganawar sirri
Ta kuma bayyana kananan hukumomin da lamarin ya shafa kamar haka: Soba, Makarfi, Giwa, Chikun, Sabon Gari, Zaria, Kaduna Arewa, Kachia da kuma karamar hukumar Jaba.
A cewar ta ,Sauran sun hada da; karamar hukumar Kubau, Lere, Sanga, Birnin Gwari, Kaduna ta Kudu, Kudan, Igabi da kuma karamar hukumar Kajuru.
Kazalika ta bayyana cewa, Ma’aikatar ta, na bibiyan lamarin, kuma anfara samun saukin yaduwar cutar a jihar.
Ta ce, ” A watan Afurilu shekarar nan, an sanar da mu barkewar Amai da Gudawa a wasu kananan hukumomi, Wanda muka tura da tawar kiwon lafiya domin gwaji, kuma suka tabbatar da cewa, cutar Kwalara ce” inji ta.
“Tun wannan lokacin, munyi wa Mutum 842 magani, kuma an sallami su daga asibiti, ya yin da yanzu haka, akwai Mutum 14 da ke amsar kulawan likitoci” a cewar ta.
Ta kara da cewa, tuni Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar, ta raba magunguna domin dakile cutar, da kuma raba sinadarin Chlorine domin tsaftace ruwan sha.
A karshe ta shawarci al’umar jihar da su dunga tsaftace Muhallin su, domin kauce wa sake barkewar cutar a jihar.I