Mutane 8 aka tabbatar sun mutu, yayin da wasu 66 suka kamu da cutar Kwalara a kananan hukumomi 3 dake jihar Kogi.
Mahukunta Ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Kogi, sun bayyana kananan hukumomin da lamarin ya shafa kamar haka; Ankpa, Kogi da kuma karamar hukumar Lokoja.
Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka reshen jihar Dakta Austin Ojotu ya ce, rahotanni sun nuna cewa, wasu mutane dayawa a jihar, sun nuna alamomin kamu wa da cutar.
“Mun sami tabbacin mullar cutar Kwalara a kananan hukumomin Kogi, Lokoja, da kuma karamar hukumar Ankpa, inda mutane 66 suka kamu, 8 kuma suka mutu.” Inji shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Abun da yasa aka Dena gani na a Fim, inji Maryam Both
Kazalika ya ce, gwamnatin jihar na aiki tare da sauran mahukunta kananan hukumomi jihar, domin dakile yaduwar cutar a fadin jihar Kogi baki daya.