Daga: Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin kwalejin fasaha ta jihar Kogi da ke Lokoja sun kori dalibai 196 daga makarantar saboda rashin tabuka abin a zo a gani.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban sashin hulda da jama’a na kwalejin, Uredo Omale ya fitar a Lokoja.
Omale ya ce shugaban kwalejin, Dakta Salisu Usman ne ya sanar da korar daliban a wani taron gaggawa na hukumar ilimi ta makarantar a ranar 12 ga watan Mayu.
A cewar Usman, an amince da korar daliban 196 ne a ranar Juma’a 25 ga watan Maris, 2022.
Ta nakalto shugaban jami’ar yana shawartar sauran daliban da su guji raba hankali tare da jajircewa wajen neman ilimi yayin da suke shirye-shiryen fara jarrabawar zangon farko na shekarar 2021/2022 da aka shirya za a fara ranar Litinin 16 ga watan Mayu, 2022.
Ya ce hukumar gudanarwar Kwalejin ta dukufa wajen ganin an samar da yanayin koyo da koyarwa ga ma’aikata da dalibai.
A cewarsa, kyakkyawan aikin karatun dalibai ya samo asali ne daga kwazo da aiki tukuru da aka samu a karkashin ingantacciyar yanayin koyo, wanda cibiyar ta sanya a gaba.
Usman,yace don haka ya bukaci dalibai da su jajirce wajen karatunsu tare da kammala karatunsu kamar yadda aka tsara.
Ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake yawan samun karuwar korar dalibai daga wannan Kwaleji saboda rashin kyawun ilimi.
“Shugaban hukumar ya sake nanata cewa gwamnatin za ta ci gaba da samar da matakan da suka dace da kuma tabbatar da inganci a cikin cibiyar,” in ji sanarwar.