By Abbas Yakubu Yaura
Mako guda bayan da mahukuntan kwalejin fasaha ta jihar Kogi, Lokoja suka kori dalibai goma bisa laifin rashin da’a, hukumar ilimi ta makarantar ta sake korar wasu dalibai 15 bisa makamancin hakan.
DUBA WANNAN LABARIN: Wani Na Hannun Daman Saraki Ya Fice Daga PDP Zuwa APC Bayan Dakatar Da Shi A Jihar Kwara
Korar dalibai goma sha biyar din dai ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin da ke kula da jarabawa ta tsakiya da hukumar ilimi ta makarantar ta yi.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabar hulda da jama’a da ka’ida ta kwalejin Mrs Uredo Omale, wacce aka rabawa manema labarai a ranar Lahadi, an gano daliban goma sha biyar da saba wa sassan da suka dace na littafin bayanan dokokin daliban.
Ta ce saboda haka akwai shawarwarin da kwamitin jarrabawar tsakiya na cibiyar ya bayar na daukar matakin ladabtarwa a matsayin matakin dakile wasu anan gaba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Laifuka sun hada da yin katsalandan, da shigar da haramtattun kayan da suka dace da jarrabawar cikin dakin jarabawar da sauran su”.
Jaridar Dimokuradiyya ta lura cewa dalibai goma sha biyar da aka kora sun fito ne daga sassa daban-daban a duk azuzuwan Diploma na ND da kuma Diploma ta HND.
Shugaban cibiyar kuma shugaban hukumar Dr Salisu Ogbo Usman ya yabawa mambobin hukumar tare da jaddada kudirin hukumar na kare martabar kwalejin ta hanyar bin doka da oda.
Don haka ya gargadi daliban makarantar da su kasance masu bin doka da oda, domin kuwa ba za a bar wani dutse ba don tabbatar da cikakken doka da oda a harabar kwalejin fasaha ta jihar Kogi.