By Abbas Yakubu Yaura
An nada mataimakin shugaban kwalejin fasaha ta jihar Osun, Iree, Dr Tajudeen Odetayo a matsayin mukaddashin shugaban Kwalejin fasahar.
Hakan na zuwa ne bayan murabus din tsohon shugaban kwalejin fasaha na jihar Osun, Iree, Dr. Woye Olaniran.
Majalisar gudanarwar cibiyar ta yi nadin ne a taronta na ranar Talata.
Shugaban ma’aikata na gwamnatin jihar Osun, Dr. Festus Olowogboyega Oyebade ya ce gwamna Gboyega Oyetola ya amince da nadin mukaddashin shugaban Kwalejin fasahar.
Shugaban riko mai shekaru 62, Dr Odetayo dan asalin Ode-Omu ne a karamar hukumar Ayedaade ta jihar.
Odetayo ya yi digirin digirgir a fannin Tsare-tsaren Ilimi daga Jami’ar Ibadan, sannan ya yi digirin digirgir a fannin Kimiyyar Gudanarwa daga Jami’ar Fasaha ta Ladoke Akintola, Ogbomoso.
A wani labarin kuma
Zaben 2023: Tinubu ne ya fi dacewa da Najeriya —– Al-Makura
Sanata Umaru Al-Makura, jigo a jam’iyyar APC daga Nasarawa ya ce zabin Bola Tinubu a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki shi ne mafi alheri ga Najeriya.
Al-Makura, mamba a kungiyar ‘Think-Think of Tinubu for President’, ya yi wannan ikirarin ne a wata ganawa da kungiyoyin goyon baya daban-daban daga jihar Nasarawa domin neman dan takarar a ranar Talata, kamar yadda NAN ta ruwaito.
Tsohon gwamnan ya kira Tinubu a matsayin babban jarumi a dimokuradiyya wanda tare da sauran masu kishin kasa suka yi gwagwarmayar wajan tabbatar da dimokuradiyya a lokacin da kasar nan ta fada cikin yanayu mafi hadari.
Ya ce Tinubu ya sauya jihar Legas a matsayin gwamnanta daga 1999 zuwa 2007 wanda har tazama yadda take a halin yanzu.
“Tinubu zai yi abun da ya dace don tabbatar da doka da oda wanda ya canza jihar Legas idan aka zabe shi a zaven hekarar 2023.
Ya kara da cewa, “Ya kashe kudin sa don tabbatar da mulkin dimokaradiyya a kasar nan kuma abu ne da ya dace a zabi irin wannan a matsayin shugaban kasa,” in ji shi.
Comments 1