By Abbas Yakubu Yaura
Kwalejin Fasaha ta Captain Elechi Amadi dake Fatakwal a Jihar Ribas, ta sanar da dakatar da daya daga cikin malamanta, Tamunotonye Solomon, na tsawon watanni uku bisa zargin cin zarafin dalibai mata.
Malamin da wata daliba mai mataki karu na 200 sun yi musayar kalamai a kafafen yada labarai kan ci gaban.
Yayin da daliban suka yi ikirarin cewa malamin ya zarge ta da sace masa kudi Naira 250,000 bayan ta ki amincewa da bukatar aurensa, malamin ya bayyana zargin a matsayin bakar harkalla, inda ya ce ya kama tsohuwar budurwar tasa ne saboda ta sace masa kudi da wasu kadarorin ofis.
Sai dai hukumar gudanarwar kwalejin, a cikin wata sanarwa da magatakardar, Chris Woke, ya sanyawa hannu, ta bayyana rashin jin dadinta da faruwar lamarin tare da raba kan ta da zargin da ake yi wa malamin.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumomin Kwalejin Captain Elechi Amadi, Rumuola, Fatakwal, sun ji haushin rahoton a wasu sassan kafafen yada labarai, tare da raba kan su kwata-kwata daga zargin ma’aikacin ta Mista Tamunotonye Zoe Solomon.
“Saboda haka mahukuntan Kwalejin Amadi, Rumuola, Fatakwal, sun dakatar da Mista Tamunotonye Zoe Solomon na tsawon watanni uku daga ranar 10 ga watan Junairu, 2022 bisa zargin cin zarafin wata daliba da wasu ayyuka na rashin da’a. ga kyakkyawan sunan Kwalejin.