By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Nekede, Jihar Imo, sun hana daliban makarantar tuki a cikin harabar ta.
Makarantar a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a ta bayyana cewa daliban da suka kawo motoci makaranta suna da hazaka da dukiyarsu.
Takardar da magatakardar makarantar, B.O Dara ya sanya wa hannu ta bayyana cewa daliban da ke da motoci na iya ajiye su a wajen kofar harabar jami’ar ba za su shigo da su ba.
Sai dai hukumar gudanarwar makarantar ta bayyana cewa ma’aikatan da ke tare da katin shaida ne kadai za’a dinga barin su suna shiga harabar makarantar.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar gudanarwa a taron ta na gaggawa ta tattauna kan amfani da ababen hawa da dalibai ke yi da kuma baje kolin dukiyarsu a harabar jami’ar.
“Bayan tattaunawa sosai, hukumar ta umurci a hana daliban tuka motocin su wajen shiga harabar jami’ar.
“Ma’aikata ne kawai za’a ba su izinin shiga harabar jami’ar saboda za a tantance ma’aikatan ta hanyar gabatar da katin shaidarsu.
“Ya kamata ma’aikatan da suka rasa katin shaidar su dasu samu takardar shaida daga magatakardar. Wasiƙar shaidar dole ne ta ƙunshi hoton fasfo na ma’aikatan.
Jaridar Dimokuradiyya ta tattaro cewa “Duk wani dalibai dole ne ya kasance da katin shaidar jami’ar a koyaushe tare da su yayin da suke harabar makarantar.”