By Abbas Yakubu Yaura
Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Aminu Dabo dake Kano, ta kori dalibai 12, bisa samun su da laifin magudin jarabawa.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Abdullahi Usman ya fitar kuma aka rabawa manema labarai a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce, wasu dalibai 13 da ke matakin karatu na aji 200 na kwalejin an same su da laifuka daban-daban da suka shafi rashin da’a a lokacin gudanar da jarrabawar.
Sanarwar ta ce an kama daliban da abin ya shafa da hannu dumu-dumu suna tafka kura-kurai da rashin da’a a lokacin jarrabawar zangon karatu na biyu na shekarar 2021/2022, sabanin tsari da ka’idojin kwalejin.
Kazalika Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar kwalejin ta dauki matakin ne kan daliban da suka yi kuskure bisa ga tanadin da ke cikin littafin daliban bisa shawarar kwamitin ladabtarwa.
“Rahoto ya nuna cewa an kama daliban da abin ya shafa da hannu wajen aikata ta’asar jarabawa da kuma rashin da’a da ya saba wa tsarin kwalejin da ka’idar aiki a lokacin jarrabawar zango na biyu na 2021/2020.
“Duk da haka, hukumar ta umurci sauran daliban da aka wanke da su koma kwalejin a ranar Litinin 17 ga watan Junairu, 2022 domin ci gaba da jarabawar zangon karatun.
“Kazalika ta gargadi daliban da abin ya shafa da su nisanci harabar kwalejin domin gujewa duk wata kara da za ta iya fuskanta.”