Kwalejin Kimiyya da Fasaha na Jihar Kogi ya kori wasu dalibansa 42 bisa samun su da aikata miyagun ayyuka daban-daban.
Cikin laifuka da aka samu daliban da aikatawa sun hada da halin ɓera da satar Jarabawa da kuma kirkiro da sakamakon bogi.
Wata sanarwa mai sa hannun kakakin kwalejin Misis Uredo Omale ta ce kwalejin ya dauki matakin korar daliban ne bayan da ya bi duk sharuda da suka kamata ya bi tare da samun sahalewar hukumar gudanarwa.
Daga cikin daliban akwai dan aji na biyu a Diploma a sashen kula da harkokin kasuwanci da masu rufa masa baya da aka same su da laifin bude wata cibiyar rubuta jarabawa tasu ta kansu.
Kazalika akwai wani dalibin tsangayar ilmin kimiyar na’ura mai ƙwaƙwalwa wanda shi kuma an same shi ne da sace-sace.