Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Filato, John Dawan, a ranar Laraba ya ce za a ci gaba da karatu a ranar Litinin bayan malamai sun dakatar da yajin aikin da suka shafe watanni uku suna yi.
Dawan ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da jaridar PUNCH a Jos, inda ya ce, “Na umurci magatakardar kwalejin kimiyya da fasaha da ya rubuta takardar neman daliban da su koma makaranta nan take.
“Ba za mu so mu bata lokaci ba bayan ‘yan kungiyar sun janye yajin aikin amma za a fara laccoci daga ranar Litinin.”
Kungiyar Malaman Makarantun Kimiyya ta Kasa reshen Jihar Filato ta shelanta yajin aiki na har sai baba ta gani tare da wasu manyan makarantun jihar guda shida kan batutuwan da suka shafi jin dadinsu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Zaben 2023: Yankin Arewa Maso Yamma Nada Matukar Mahimmanci Ga Nasarar APC – Dattijo
Shugaban ma’aikatan kungiyar hadin guiwa ta malaman manyan makarantun jihar Filato Dabam Lawam, ya tabbatar wa da jaridar PUNCH cewa ta dakatar da yajin aikin a ranar Laraba.