Gwamnatin jihar Sokoto ta ce sabuwar jami’ar ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto za ta fara aiki a shekarar 2022.
Al-Mustapha Ali, babban sakataren ma’aikatar ilimi mai zurfi na jihar ya bayyana hakan a ranar Juma’a, lokacin da jami’an ma’aikatar suka bayyana a gaban kwamitin majalisar dokokin jihar kan ilimi mai zurfi domin kare kasafin kudin shekarar 2022 da za mu shiga.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa ya rawaito cewa, a ranar 28 ga watan Disamba, 2020, Gwamna Aminu Tambuwal, ya sanar da daukaka darajar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari mai shekaru 51 zuwa jami’ar ilimi.
A cewar Mista Tambuwal, an yanke hukuncin ne bisa ga kishin Kwalejin. “Kwalejin wanda aka samad da ita da hangen nesa, kirkire-kirkire da kwarewar jagoranci suna da alaƙa da kakanninmu a tarihi sama da ƙarni biyu,” in ji shi.
A cewar Ali, sabuwar kwalejin kimiyyar likitanci ta jami’ar jihar ita ma za ta fara ayyuka a wannan shekarar. “Sabuwar Jami’ar Ilimi za ta karfafa horar da isassun ma’aikata da za su kula da bangaren ilimi na jihar.
“Kwalejin kimiyyar likitanci ita ce ta samar da ƙarin ma’aikata don cibiyoyin kiwon lafiya da asibitocinmu. “Kayan aikin jinya sun hada da: Sabon Asibitin Koyarwa na Jami’a, wanda ake kan gina shi da kuma manyan asibitocin da aka inganta a fadin jihar,” inji shi.
Mista Ali ya kara da cewa gwamnatin jihar ta samar da isassun tanadi domin fara karatun digiri na farko da na biyu a jami’ar jihar sama da 50.
“Mun shirya tsaf don tabbatar da cewa duk kwasa-kwasan da ake bayarwa a babbar jami’a mallakar gwamnatin jihar sun samu shaidar da ake bukata daidai da lokacin da ya kamata,” in ji shi.
Shugaban Kwamitin Sule Romo (PDP- Tambuwal West), ya tabbatar da cewa Majalisar za ta cigaba da tallafa wa ma’aikatar don cimma nasarorin da take so a fannin ilimi.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar ta jaddada kudirinta na kammalawa tare da fara ayyukan da suka gada a karkashin ma’aikatar lafiya ta jihar a shekarar 2022.
Dakta Ali Inname, kwamishinan lafiya na jihar ne ya bayyana hakan a lokacin da jami’an ma’aikatar suka bayyana a gaban kwamitin majalisar kan harkokin lafiya domin kare kudirin kasafin kudin shekarar 2022.
A cewar Mista Inname, ma’aikatar ta samu nasarori da dama a wannan shekarar ta 2021 kuma za ta ci gaba da bin wannan hanya domin tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya a jihar.
“A shekarar 2022, za mu ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da nasarar ayyukan da muka bari a fannin kiwon lafiya.
“Gwamnatin jihar za kuma ta tabbatar da inganta wasu manyan asibitoci zuwa asibitocin kwararru,” in ji shi.
Shugaban Kwamitin, Ibrahim Sarki (PDP- Sokoto North II), ya yabawa gwamnatin jihar bisa fifikon fannin kiwon lafiya a jihar.
Ya kuma ba da tabbacin cewa kwamitin zai ci gaba da hada gwiwa da ma’aikatar domin tabbatar da isar da ayyukan kiwon lafiya na duniya ga al’ummar jihar.
NAN