Wani magidanci mai shekaru 47 mai suna Alhaji Musa Tsafe dake karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara ya ki sakin jikarsa da ya aura shekaru 20 da suka gabata.
Ya dauki matakin kin sakin ne bayan an sanar da shi haramcin irin wannan hadaka, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito a yau Lahadi.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa matar mai shekaru 35, mai suna Wasila Isah Tsafe, ta haifi ‘ya’ya takwas a cikin auren shekaru 20 da suka yi.
Sai dai wani sabon salo ya kara shiga cikin rayuwar auren ma’auratan bayan an sanar da majalisar masarautar Tsafe kan haramcin auren, wanda hakan ya biyo bayan umarnin Musulunci.
Shugabannin al’umma da malaman addinin musulunci ne suka gayyace su domin su bincikar lamarin, kuma bayan bincike aka gano cewa auren ya sabawa doka.
Malaman addinin musulunci sun shawarci Tsafe da ya saki matarsa amma ya ƙeƙashe ƙasa wajen cewa ba zai yi haka ba.
An kuma kara da cewa malaman sun amince da halaccin ‘ya’yan da suka haifa, amma sun dage cewa auren ba shi da hakki tunda an kawo wa ma’auratan matsalar.
Bayan dagewar nasa ne kwamitin Hisbah na karamar hukumar Tsafe ya dauki nauyin shari’ar inda ya shigar da kara a gaban wata babbar kotun karamar hukumar daga bisani kuma, babbar kotun shari’a.
Kotun kolin shari’ar musulunci ta dage sauraron karar zuwa ranar 21 ga watan Yuli.
A halin da ake ciki kuma, Tsafe, ya kai karar Sheikh Dahiru Bauchi ne bayan ya koka da cewa shiri ne na shigar da akidar Izala a cikin lamarin.
Amma an rawaito cewa Sheikh Bauchi ya sake jaddada matsayin malaman Tsafe a baya, amma ya dage da zama da matarsa.