By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan Muhalli na Jihar Kogi, Cif Victor Adewale Omofaiye a ranar Lahadin data gabata ya tsallake rijiya da baya a yunkurin da wasu sukayi na sace shi a tsakanin Oke-Ijumu da Iyara a karamar hukumar Ijumu.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa A cewar wani ganau wanda ya nemi a sakaya sunansa yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma a lokacin da yake kan hanyarsa ta daga mahaifarsa, Ekinrin Adde inda ya halarci wasu bukukuwa da aka gudanar a yankin.
Sai dai kuma shaidun gani da idon ya yi nuni da cewa an yi garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba a harin.
Kwamishinan ya shaida wa manema labarai a gidan rediyon jihar cewa har yanzu ba a tantance ‘yan bindigar ba da adadinsu ya kai 20 sun yi masa kawanya da bindigogi.
Kazalika Omofaiye ya bayyana cewa ya dauki matakin gaggawar bayan da mai taimaka masa kan harkokin tsaro ya shiga tsakani wanda ya kore su amma ya samu harbin bindiga a kafarsa.
Olu Adde na Ekinrin, Oba Anthony Bamigbaiye Idowu ya tabbatar da harin a cikin wani gajeren sako.