Kwamishinan matasa, wasanni, zamantakewa da cigaban al’umma na jihar Yobe, Goni Bukar Lawan, ya rasu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar Damaturu zuwa Kano.
Wanda lamarin ya ritsa da shi tsohon dan majalisar wakilai, mai wakiltar Bursari, Geidam, da Yunusari na tarayya ya mutu a yammacin ranar Talatar nan.
An ce ya halarci jana’izar abokinsa, Daraktan Kudi na NNPC, Hassan Gambo, a ranar Talatar da yamma a Damaturu kafin ya yi tafiya zuwa Kano inda ya yi hatsarin a kusa da garin Dambam a jihar Bauchi.
Babagana Mai-Modu, Babban Daraktan Hulda da Yada Labarai na Gwamna Mai Mala Buni, ya tabbatar da faruwar lamarin ga gidan Talabijin na Channels a wata tattaunawa ta wayar tarho.
Ya ce an ajiye gawar kwamishinan a dakin ajiyar gawa na asibitin koyarwa na jami’ar jihar Yobe Damaturu.
Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa wasu abokansa biyu da ke tare da shi a lokacin hadarin, suna karbar magani a daya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya a jihar.