Daga: Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, CP Sikiru Akande, ya bukaci duk masu amfani da ababen hawa da su mayar da lambobin SPY zuwa hedikwatar ‘yan sanda da ke Yola.
Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan (PPRO), SP Suleiman Nguroje ya sanya wa hannu, ta nuna cewa umurnin wani mataki ne na mutunta haramcin da babban sufeton ‘yan sanda yayi amfani da lambobin SPY a fadin kasar nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: https://dimokuradiyya.com.ng/tikitin-tinubu-da-shettima-ganduje-yayi-kakkausan-martani-ga-babachir-lawal-kan-ajanda-musuluntar-da-yan-najeriya/
PPRO yace CP Akande ba zai kyale masu karya doka ba ko kuma ya amince da bata gari da ka iya dagewa a yi amfani da lambobin spy.
Sanarwar ta ce ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro za su kwace irin wadannan lambobin daga hannun duk wanda aka samu yana amfani da su.
“Shugaban ‘yan sandan ya kara da umurci jami’an ‘yan sanda na yanki, kwamandojin aiki da kwamandojin yanki da su gaggauta aiwatar da wannan umarni,” in ji sanarwar.
Ya kara da cewa rundunar da ta kunshi dukkan jami’an tsaro za ta zagaya lungo da sako domin tabbatar da bin ka’idar.
A wani labarin kuma Misis Yetunde Adeyanju, kwamishiniyar ma’aikatar tsare-tsare da raya birane ta jihar Ondo, ta yi murabus daga mukaminta a gwamnatin gwamna Oluwarotimi Akeredolu.
Bayan da aka dauke ta a ranar Litinin daga ma’aikatar ruwa da tsaftar muhalli zuwa ma’aikatar tsare-tsare da raya birane, Misis Adeyanju ta mika takardar murabus din ta sa’o’i bayan da aka mayar da ita wata ma’aikatar.
A cikin kwafin takardar murabus din ta da majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta samu labari Adeyanju ta yabawa Akeredolu bisa damar da aka ba ta na yiwa al’ummar jihar Ondo hidima.
A cewarta, murabus din na da nasaba ne da wani hukunci na kashin kanta da aka yanke na yin bincike a kan wasu ayyuka a wajen siyasa.
Abin da ke cikin wasikar ya ce, “Na yi murabus daga mukamina na kwamishiniya a Jihar Ondo ba tare da bata lokaci ba.
“Duk da haka, ina godiya a gare ku bisa ga dama ta zinariya da aka ba ni na ba da gudummawa, ci gaban jihar mu, musamman ta hanyar samar da ruwan sha na Kamomi Aketi.
“Kun ba ni dandalin kuma ina alfahari da cewa na yi amfani da shi da kyau don amfanin bil’adama.”