By Abbas Yakubu Yaura
Rundunar Jami’an tsaro da suka hada da kwamishinan ‘yan sandan jihar Kaduna, Abdullahi Mudassiru, tare da kwamandan sojojin Najeriya shiyya ta daya Garrison, Birgediya Janar UT Opune da Wakilin Daraktan Hukumar DSS na Jiha, Mista SG Shinkafi wadanda suka hadu dan zuwa wurin da harin ‘yan bindigar ya afku a Karamar Hukumar Khacia.
Kazalika da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida, Samuel Aruwan, wanda shine ya jagoranci sauran tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan matafiya a Kurmin Kare, dake karamar hukumar Kachia ta Jihar Kaduna.
Harin dai na Kurmin Kare wanda ya yi sanadin mutuwar mutum guda tare da yin garkuwa da wasu da ba a bayyana adadinsu ba.
Bayanan hakan na kunshe ne cikin sanarwar da ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Jihar Kaduna tafitar.