By Abbas Yakubu Yaura
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, Abiodun Alabi, ya bayar da umarnin a tsaurara matakan tsaro a jihar.
An ba da umarnin ne ga dukkan kwamandojin yankin da jami’an ‘yan sanda na shiyyar da ke jihar.
Hakan ya biyo bayan dakatarwar da kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa ta yi wa shugaban kungiyar reshen jihar Legas, Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo.
CP Alabi, yayin wata tattaunawa da gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis, ya ce an bayar da umarnin tura jami’an a dukkanin wuraren shakatawa na motoci a fadin kasar nan.
Shugaban ‘yan sandan ya ce wannan umarni ya zama dole domin dakile duk wani tashin hankali da ka iya tasowa a jihar daga rikicin da ya dabaibaye kungiyar ta NURTW.
Da yake kira ga kwamandojin yankin da DPOs da su ci gaba da kasancewa a yankunansu, CP Alabi ya ba mazauna Legas tabbacin samun isasshen tsaro na rayuwa da dukiyoyi.
An dakatar da MC Oluomo ne bisa zarge-zargen rashin da’a, rashin biyayya, da kuma tunzura ‘yan kungiyar reshen jihar a kan kwamitin koli.