Kwamishinar Muhalli da gandun Daji ta jihar Gombe Dr. Hussaina Danjuma Goje ta sanar da ajiye muƙamin ta na matsayin Kwamishina.
Dr. Hussaina Goje ta bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da ta gudanar da nufin sanar da ajiye muƙamin na ta.
Ta kara da cewa ta ajiye aikin ne bisa raɗin kanta, ba wai dan wani dalili na rashin jin dadi ba a karkashin gwamnan jihar ta Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya.
DUBA WANNAN LABARIN: Bukola Saraki Ya Soki Hukuncin Garƙame Majalisar dokokin jihar Filato
Dr. Hussaina a karshe ta kuma godewa Gwamna Muhammadu Yahaya bisa zabar ta domin zama daga cikin yan majalisar zartarwar jihar, wanda ta ce wannan ma wata dama ce da ya bata tare da yi masa godiya kan hakan.