A ci gaba da kokarin sasanta rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, a yau Talata ne kwamitin amintattu na jam’iyyar zai gana da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike a Fatakwal.
Za a gudanar da taron ne a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal da karfe 12 na rana.
Wani babban jami’in jam’iyyar a jihar da bai so a ambaci sunansa ba ya tabbatar wa da wakilinmu a safiyar ranar Talata.
KARANTA ANAN: Donald Trump Yayi Karar CNN, Tare Da Neman Wasu Kudi A Matsayin Diyya
Ana sa ran mutanen Wike da gwamnonin Enugu, Abia, Benue, Oyo, da kuma wasu manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar za su halarci taron.
Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Gwamna Wike da wasu gwamnonin yankin Kudu sun kauracewa yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar.
Don haka, ana sa ran za a tattauna a taron da nufin samun matsaya guda don kwantar da hankalin Wike da mutanensa yayin da zaben 2023 ke kara kusantowa.
Gwamna Wike da wasu takwarorinsa hudu, wadanda a yanzu ake kira da manyan gwamnoni biyar, sun kulla kawance domin neman daidaito da adalci a jam’iyyar.
Babban abin da suke bukata shi ne shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorcha Ayu, ya yi murabus, domin share fagen ganin dan kudu ya gaje shi tun da Atiku, dan Arewa, shi ne ke da matsayin shugaban jam’iyyar.
A wani labarin kuma: Ƙwararru sun koka rashin zuba kuɗaɗe ga Bincike a ɓangaren lafiya a Najeriya
Kwararru sun ce rashin zuba kudade a ɓangaren lafiya na kawo cikas ga bincike a Najeriya.
Sun bayyana hakan ne jiya a Abuja a yayin taron shekara na 6 na kungiyar NISA da aka yi mai taken ‘Dorewar Shirye-shiryen Aiwatarwa & Bincike’.
Kwararrun, wadanda suka hada da masu bincike, masu tsara manufofi da masu aiwatar da shirye-shiryen kiwon lafiyar jama’a sun ce akwai bukatar a magance tazarar ilimi tsakanin masu tsara manufofi da masu bincike don tabbatar da aiwatar da sakamakon bincike mai inganci a kasar.