Kwamitin Hisba ya kori wani babban jami’i a Kano
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta dakatar da nadin daya daga cikin manyan jami’anta, Sani Nasidi Uba, wanda aka fi sani da Sani Remo saboda “haifar da abin kunya ga rundunar.”
Kwamitin da Kwamandan Janar, Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina ya kafa, ya tuhumi Uba da samun sa da wani mummunan aiki.
Uba, wanda aka san shi a sahun gaba wajen kame karuwai da sauran ‘yan mata marasa gaskiya, an kama shi ne a cikin watan Faburairun bana tare da wata matar aure a wani dakin otal da ke yankin Sabon Gari a babban birnin jihar.
Daga nan sai jami’in ya fadawa rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano cewa matar da ake magana a kai‘ yar dan uwansa ce wacce take samun matsala da mijinta.
A cewarsa, ya ajiye ta a dakin otel har zuwa lokacin da za a warware matsalolin ne, Inji shi.