By Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin jihar Oyo ta samar da tsarin sa ido da magani yayin da zazzabin Lassa ya bazu zuwa yankin Oke Ogun da ke jihar.
Kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Bode Ladipo, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Litinin, ya bayyana cewa cutar ta kashe wasu mazauna yankin.
Ya ce jihar ta samar da tsarin sa ido a kananan hukumomin domin dakile cigaba da yaduwar cutar.
Ladipo ya ce, “Lamarin ya ja hankalin ma’aikatar da aka samu rahoton mace-mace a karamar hukumar Iwajowa ta jihar Oyo a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, 2022. An ce wadanda suka mutun na da alaka da zazzabin na lassa, alamun ciwon ciki da kuma kumburin wuya.
“Wannan ya bai wa wata babbar tawagar bincike karkashin jagorancin Kwamishinan Lafiya damar ziyartar karamar hukumar a ranar Alhamis, 13 ga Janairu, 2022 don tantance halin da ake ciki tare da bayar da tallafin da ya dace don dakile duk wani kamuwa da cutar.
“Tawagar ta kunshi manyan jami’an ma’aikatar da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jiha da kuma hukumar lafiya ta duniya.
“Ziyarar farko da aka kai babban asibitin jihar da ke Iwere lle ta nuna cewa an samu karuwar adadin wadanda aka kawo daga yankin Gaa Agbaruru tare da tabbatar da mutuwar mutane biyu a wurin. Daga nan ne aka jagoranci tawagar zuwa Gaa Agbaruru, wani matsugunin Fulani da ke unguwar Iwere ta karamar hukumar inda wadanda suka kamu da cutar suka fito.
“An lura cewa akwai lokuta da alamun da aka ambata a sama amma suna murmurewa. An kuma tabbatar da cewa lallai akwai mu’amala mai yawa tsakanin mazauna garin da Beraye da Jemagu. Bugu da ƙari, an lura da ƙalubalen samun ruwan sha.
“An dauki samfurin jini daga mutanen da suka warke tare da samfurin ruwan yankin. An aika da waɗannan samfuran zuwa dakin gwaje-gwaje na bincike na ƙasa don zazzaɓin jini da ke Abuja don bincike da tabbatarwa.
“Sakamakon binciken da aka yi daga dakin gwaje-gwaje na Reference ya samu a yau, 17 ga Janairu, 2022 tare da biyu daga cikin samfurori 10 da aka gwada sun kamu da zazzabin Lassa.
“Saboda haka, ma’aikatar ta sake sanya alluran rigakafin cutar zazzabin Lassa da na’urorin kariya ga ma’aikatan lafiya a Iwere lle da Iganna. Ilimin kiwon lafiya da tsaftar muhalli na gudana a halin yanzu a cikin al’ummomi.
“An kara inganta tsarin sa ido na jihar a dukkan kananan hukumomin jihar.
“Za a mika wadanda ake zargi zuwa Asibitin Gwamnati mafi kusa don samun kulawa kyauta kuma mai inganci.”