Kwamitin lura da wuraren hada magunguna dake karkashin ma’aikatar kiwon lafiya ta jiha ta rufe wasu cibiyoyin hada magani da kuma shagunan sayar da magunguna dake cikin Kano.
Shugaban Kwamitin wanda kuma shine Daraktan bangaren hada magani na ma’aikatar kiwon lafiyan jihar, Pharmacist Abdu Umar Madaki ne ya jagoranci tawagar Kwamitin zuwa aikin rufe cibiyoyin da shagunan kan rashin bin ka’idar hadawa da sayar da magunguna.
Pharmacist Abdu Madaki ya kara da cewa dole ne duk wani kamfanin hada magani ko shagunan sayar da magunguna dake cikin jihar Kano, su kasance suna da rajistar izinin yin hakan a karkashin Majalisar masu hada magunguna ta Nijeriya ta jihar Kano.
Kamfanin hada magunguna da shagunan sayar da maganin da aka rufen, sun hada da FEDEX LOGISTIC COMPANY, AGARY PHARMACEUTICAL LTD da kuma HAUWA’U PATIENT MEDICINE SHOP dake cikin babban asibitin Sheikh Jeddah.
Wadannan cibiyoyi da shaguna ba za’a budesu ba har sai sun bi dokokin da Kwamitin ya shimfida da ka’idojin ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar.