Kwamitin Tsare-tsare na Ganduje ya jaddada wa mambobin APC ƙarfin gwuiwar shirya Babban Taro — Cewar Buni
Shugaban Kwamitin Ruƙo da Tsare-tsaren Shirya zaɓen Shuwagabannin APC na Ƙasa kuma Gwamnan Jahar Yobe Mai Mala Buni, yace aikace-aikacen Ƙaramin Kwamitin Shirye-shirye ya bayar da wani tabbaci ga mambobin jami’iyyar cewa, an shirya domin Jam’iyyar data fi kowace girma a Afirka ta Shirya Babban Zaɓen Shuwagabannin ta a ranar 26 ga watan Maris.
Dayake Karɓar bayanai daga Shugaban Ƙaramin Kwamitin kuma Gwamnan Jahar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da Mataimakin sa da sauran Mambobin Kwamitin a gidan sa dake Abuja a daren ranar Asabar, Buni ya Bayyana cewa Kwamitin ya tabbatar wa da Mambobin Jam’iyyar cewa za’a gudanar da zaɓen a ranar da aka sanya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Gwamna Sani-Bello Ya Ziyarci Sansanin ‘Yan Gudun Hijira Na Gwada, Ya Gargadi ‘Yan Bindiga
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaru na Jahar Kano, kuma mamba a Kwamitin Malam Muhammad Garba ya fitar, inda ya naƙalto Buni na cewa Jam’iyyar na shirya Babban zaɓen ne duniya na kallo, wanda hakan ke buƙatar haɗin kai da ƙoƙari a tsakanin mambobin.
Mai Mala Buni ya yabawa Kwamitin, wanda yace sunyi aiki mai kyau wajen tabbatar dacewa Jam’iyyar ta gudanar da Babban taron.
Buni ya ƙara dacewa Ƙaramin Kwamitin shine mafi amfani baya ga Kwamitin Ruƙon ta la’akari da irin mahimmancin sa, wanda hakan ya sanya aka ɗora Gwamna Ganduje ya jagorance shi da waɗanda suka yi zarra wajen kawo cigaba a wuraren su.
Ya kuma yi kira ga Kwamitin da yayi aiki kafaɗa da kafaɗa da Kwamitoci, musamman da Ofishin Shirye-shirye na Fadar Shugaban Ƙasa Abuja, ta la’akari da cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo zasu halarci taron.
Tunda Farko, Shugaban Ƙaramin Kwamitin Tsare-tsaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace ya ɗauki Mata da Maza su zamanto masu shirye-shirye da kuma masu nunawa mutane hanyoyi wato-Ushers, kuma yanzu haka suna karɓar horo a matsayin wani nauye-nauyen kwamitin.
Yace Kwamitin yana kuma aiki domin ɓullo da wani tsare-tsaren yadda za’a samu nasarar shirya Babban taron Jam’iyyar.
Ganduje ya godema Shugaban Kwamitin Ruƙo da Tsare-tsaren Shirya zaɓen Shuwagabannin Jam’iyyar APC na Kasa da sauran Mambobin Kwamitin da suka yi alƙawarin yin aiki da Babban Kwamitin Tsare-tsaren domin samun nasarar shirya Babban zaɓe na Ƙasa.
Sauran Mambobin Kwamitin sun haɗa da Sanata Godswill Akpabio, da Tsohon Gwamnan Jahar Akwa Ibom kuma Ministan Harkokin Niger Delta Sanata Adeleke Mamora, da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jahar Lagos, kuma Ƙaramin Ministan Lafiya Rep. Hafizu Kawu, da Ɗan Majalisar Wakilai na Tarauni, Kuma Shugaban ɓangaren shirye-shirye na APC Abdullahi Shu’aibu da sauran su.
Comments 1