By Abbas Yakubu Yaura
Hukumomin zaben kasar Somaliya sun nada sabon shugaba bayan korar tsohon shugaban da ake zargi da hannu a zabukan.
Sanarwar kwamitin aiwatar da zaben Somaliya (FEIT) ya biyo bayan barazanar takunkumin Amurka idan kasar ta tsallake sabon wa’adin ranar 25 ga watan Fabrairu na gudanar da zabe.
“Dan takarar da ya sha kaye ya samu kuri’u 11 yayin da dan takara na biyu Muse Gelle Yusuf ya samu kuri’u 14. Saboda haka daga yanzu shi ne sabon shugaban kwamitin aiwatar da zaben tarayyar Somalia (FEIT)”, in ji mataimakin shugaban FEIT, Mowlid Matan Salad.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wa’adin shugaba Mohamed Abdullahi Mohamed, wanda aka fi sani da Farmajo, ya kare ne tun a watan Fabrairun shekarar 2021.
An tsawaita wa’adin aikinsa a cikin watan Afrilu wanda ya haifar da tashin hankali a Mogadishu, babban birnin kasar.
Shugaban mai jiran gadon ya tabbatar da aniyar sa na gudanar da binciken da aka dade ana jira.
“Game da jinkirin da aka dade ana yi da kuma sabon wa’adin zabe, wanda kuma babban nauyi ne a kanmu, mun kuduri aniyar fara gaggawar cika wannan sabon wa’adin, in Allah Ya yarda,” in ji Musa Gelle Yusuf.
Kasar Somaliya na cikin wani mawuyacin hali na tada kayar baya na kungiyar Al-Shabaab.
A ranar Laraba, wani harin kunar bakin wake da aka kai da wata mota a babban birnin kasar ya kashe akalla mutane hudu.