An sake yi katari babu wanda cutar coronavirus ta kashe a Najeriya a daren Juma’a, kamar yadda lamarin yake a Alhamis, a yayin da adadin wadanda cutar ta kashe a kasar ya kai dubu 2 da 27.
Hukumar yaki da cututtuka ta kasar ce ta sanar da haka a daren na juma’a.
Babu wanda wannan cuta ta kashe a wannan mako, wato babu wanda wannan cuta ta aika lahira a cikin sa’o’i 24, zalika babu wanda ya mutu sakamakon harbuwa da cutar a ranar Lahadi da ta gabata.
Bugu da kari, an jera makonni ana samun adadin wadanda cutar ke harba yana yin kasa,.
adadin wadanda ke harbuwa da cutar ya ci gaba da raguwa a Kasar a cikin makonni 3 da suka wuce, inda mutane 130 kawai suka harbu da cutar a daren Juma’a.
fiye da kashi 2 cikin 3 na mutane 161,000 suka harbu da cutar a Najeriya sun murmure sarai bayan da aka yi musu magani.
Bayanan da hukumar yaki da cututtuka ta kasar ta wallafa na nuni da cewa mutane 147,581 da suka kamu da cutar ne suka warke.