A kalla kasa da sa’o’i 24 kenan bayan fashewar wani bututun iskar gas da yayi sanadiyar salwantar rayukan Mutane uku, wani bututun ya sake fashewa yayin da al’ummar musulmi ke gudanar da shagulgular Sallah.
Fashewar ta farko ta auku ne a shekaran jiya Laraba inda ta kona mutane uku kurmus, yayin da wasu hudu kuma suka jikkata a birnin Abekuta na Jihar Ogun.
Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Ogun ta tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda ta ce mutum guda da ya samu rauni na chan asibiti rai a hannun Allah.
Cikin wata sanarwa daga Daraktan hukumar Injiniya Fatai Adefala ya ja hankalin mutane da su rika kaffa-kaffa a yayin da suke mu’amala da abin da ya shafi ganyen wuta.