- Kwanaki biyar kafin barinsa ofis shugaba Buhari yayi wani sabon nadi.
- Shugaba Buhari ya amince da nadin Garzali Muhammed Abubakar a matsayin babban sakataren asusun bunkasa noma na kasa.
- Buhari ya nada akalla mutane bakwai a ofishin shugaban da mambobin kwamitin kungiyar.
A ranar Alhamis ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Garzali Muhammed Abubakar a matsayin babban sakataren asusun bunkasa noma na kasa,Daily Post ta rawaito.
Hakan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar.
KARANTA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Gwamnan APC Ya Rusa Majalissar Kwamishinoninsa, Ya Kori Dukkan Hadimansa
A cewar sanarwar, Buhari ya kuma amince da nadin akalla mutane bakwai na ofishin shugaban da mambobin kwamitin kungiyar.
Wadanda Aka Nada Sun Hadar da
Misis. Aduke Bamidele Hussain – shugaba
Dakta Hussaini I. Mohammed (Wakilin Arewa ta Tsakiya)
Mr. Mohammed Umar (Wakilin Arewa maso Yamma)
Mr. Abdulsalam Yahaya Ahmed (Wakilin Arewa maso Gabas)
Misis Stella Uzokwe (Wakiliya ta Kudu maso Gabas)
Mr. Stephen Ikata (Wakilin Kudu maso Kudu)
Mr. Olufunlayo Oluwole Faloye (Wakilin Kudu maso Yamma).
A wani labarin kuma, Matatar Man Dangote Zata Samar Da Dala Biliyan 21, Matasa Sama Da 100,000 Za su Sami Aiki
Shugaban rukunin kamfanin Dangote wato Aliko Dangote ya bayyana cewa sabuwar matatar Mansa mai tace Lita 650,000kowace rana, za ta dauki matasan Najeriya 100,000 aikin yi da kuma samar da sama da dala biliyan 21, don ceton wa kasar nan makudan kudaden da za a yi amfani da su wajen shigo da mai. Kamar yadda Independent Post ta ruwaito.
A cewar hamshakin dan kasuwar, kamfanin yanzu yana da ma’aikata sama da 33,000.