Mutuwar ta Jakada Du Wei na zuwa ne kwanaki kadan bayan ziyarar Sakataran harkokin wajen Amurka a Isra’ila Mike Pompeo wanda ya gargadi kasar da ta daina saka jari a Chana.
Dw Hausa sun labarto cewa; Majiyoyin tsaro a Isra’ila sun ce an taras da gawar Jakadan Chana a haramtacciyar kasar Isra’ila a gidansa da ke kusa birnin Tel-Aviv.
Du Wei dan shekaru 57 tsohon Jakadan Chana ne a Ukraine wanda aka nada shi Jakada a cikin watan Maris da ya gabata a haramtacciyar kasar Isra’ila, ya mutu ne a gidansa dake a Herziliya kusa da Tel-Aviv.
Ya zuwa yanzu hukumomin sun ce ba su da masaniya a game da mutuwar jami’in diplomasiyar wanda iyalansa ba tare suke da shi ba a can.