Dan takarar gwamna na jam’iyyar PRP, Farfesa David Bamgbose ya rasu.
Mutuwar Bamgbose na zuwa ne kwanaki bakwai bayan da ya lashe tikitin jam’iyyar PRP don zama dan takarar gwamna a jam’iyyar.
Ya kasance dan takarar sanata a jihar Ogun ta Yamma a karkashin jam’iyyar PDP kafin ya tsaya takarar Mista Ganiyu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wasu Jiga-Jigan Jam’iyar APC Da Tarin Magoya Bayansu Sun Koma PDP A Sokoto
A karshen makon da ya gabata ne Bamgbose ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP, inda ya yi zargin cewa matakin da ya dauka na ficewa daga takarar sanatan ba bisa son rai ba ne.
DAILY POST ta samu cewa dan asalin jihar Yewa ta Arewa ya rasu ne a asibitin jihar dake Lantoro Abeokuta bayan gajeruwar rashin lafiya a ranar Juma’a.
Mataimakin babban Fasto na Cocin Peace and Love, Mista Olayemi Oduntan, ya tabbatar wa manema labarai rasuwarsa.
A cewar Oduntan, dan takarar gwamnan yana wani asibiti a Olomore, inda aka tura shi babban asibitin tarayya da ke Idi-Aba na garin, Abeokuta.
“Mun zabi asibitin jihar, Lantoro saboda gaggawa kuma an kwantar da shi a sashin gaggawa inda aka sanya ma shi na’urar da ke taimakawa mutum wajen Numfashu har zuwa ranar Juma’a.
“Na dawo asibiti a safiyar yau, na same shi yana numfashi da kyar. Sai na fita na kawo masa wasu magunguna da aka rubuta abaya” Oduntan ya bayyana.
Har zuwa rasuwarsa, Bamgbose ya kasance shugaban Kwalejin Ilimi ta Yewa da ke Abeokuta.
Mamacin mai shekaru 54 a duniya ya rasu ya bar matarsa Mary Bamgbose da ’ya’ya shida.
A WANI LABARIN KUMA: Mun Baiwa Mutane 6,000 Tallafin Naira 20, 000 Kowannensu A Jihar Katsina—Sadiya Umar Farouq
Akalla mutane 6,000 ne suka karbi Naira 20,000 kowannensu a matsayin tallafin kudi a Katsina a wani bangare na kokarin gwamnatin tarayya na rage radadin talauci a tsakanin talakawa da marasa galihu a kasar nan. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
Hakazalika, sama da iyalai 1,000 a jihar ne suka ci gajiyar abinci da kayan abinci a matsayin tallafin da gwamnatin tarayya ke yi ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.