An yi ta ce-ce-ku-ce a Kano a ranar Asabar yayin da wasu manya suka mamaye masallacin Aliyu Bin Abi-Dalib domin halartar daurin auren Hafsat, diyar Akanta-Janar na Tarayya, Alhaji Ahmed Indris.
Manyan baki da suka halarci bikin sun hada da ministan tsaro Bashir Magashi; Karamin ministan kasafi da tsare-tsare na kasa, Clem Agba; da Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) Corps Marshal, Bobboyi Oyeyemi; tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna.
Farfesa Sambo Junaid, Walin Sokoto ya tsaya a matsayin waliyin amarya yayin da aka biya Naira 100,000 a matsayin kudin sadaki.
Da yake jawabi jim kadan bayan daurin auren, Idris ya godewa dukkan wadanda suka halarci bikin, ya kuma yi kira ga sabbin ma’auratan da su zauna cikin soyayya.
“Muna musu fatan Alheri da kuma addu’ar Allah ya yi musu jagora a sabon gidansu kasancewar su ‘yan uwa ne daga yau. Wataƙila ba da daɗewa ba za su haifi ɗa, mace ko ma tagwaye. Don haka ina fata za su zauna lafiya kuma ba za su bari wani na uku ya shiga cikin aurensu ba, ko da ni ne,” in ji AGF.