By Ishaq Dabai
Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kaddamar da asibitin Amana Sanatorium, wani asibitin gyaran miyagun kwayoyi a Kano a yayin tunawa da bikin cikarsa shekaru 65 a duniya.
Cibiyar mai dimbin manufofi, wacce take a ƙauyen Jido dake ƙaramar hukumar Binni a kan babbar hanyar Kano-Wudil, tana da sashen kula da ɓacin rai da cibiyar gyarawa.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin, Kwankwaso yace an kafa cibiyar gyara ne saboda mutanen dake da matsalar muggan kwayoyi suna buƙatar babban kulawa ta musamman.
“A baya, gwamnatin tarayya da na jihohi ne ke ba da cibiyoyin gyara da sarrafa su amma an yi watsi da wadannan cibiyoyin,” in ji shi.
Sannan yace a cibiyar, wadanda ke fama da muggan kwayoyi za su sami halartar likitocin tabin hankali, ma’aikatan jinya na likitanci, kwararrun likitocin asibiti, masana zamantakewa, masu ilimin halin kwakwalwa, masu ba da shawara da masu koyar da addini.
A cewarsa, za a yi wa mutanen dake da alaƙa da miyagun ƙwayoyi a cibiyar don basu damar dawowa cikin rayuwarsu ta yau da kullun.