Madugun Ɗarikar Kwankwasiyya kuma jagoran jam’iyyar NNPP na kasa Rabi’u Musa Kwankwaso ya sake kai wata ziyarar bazata gidan sanatan Kano ta tsakiya Ibrahim Shekarau.
Kwankwaso dai ya kai ziyarar ne yau da yamma, a gidan Sanatan dake Mundubawa a kwaryar Kano, da nufin tattaunawa da shi kan batun komawar sa Jam’iyyar.
Wannan dai ba itace ziyarar farko da Kwankwason ya kaiwa Shekarau ba, a yan kwanakin nan da nufin tattaunawa da sanatan.
A baya dai Shekarau ya sanar da cewa zai sanar da ficewar sa da APC zuwa NNPP a Jiya Litinin, amma har kawo yau shiru kake ji.
Wata Sanarwa daga ɓangaren sanatan ta bayyana cewa a gobe ne zai sanar da ficewar ce, daidai lokacin da bangaren Gwamna Ganduje ke kokarin shawo kansa.
Siyasar Kano dai yanzu haka na ci gaba da daukar Dumi, musamman yadda jam’iyyar NNPP ke ci gaba da samun magoya baya daga APC d PDP.